A Daina Sa Shugaba Buhari A Rikicin Sarautan KanoA DAINA SA SHUGABA BUHARI A RIKICIN SARAUTAN KANO.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, baida hanu kota wace hanya cikin tube rawanin Sarki Muhammadu Sanusi na biyu, daga mukamin Sarkin Kano, Dukkan irin wannan rade radin ba Gaskiya ba ce, kage ce kawai don cimma wani bukata ta Siyasa.

Ko a Tarihi Shugaba Buhari bai taba katsalan dan a harkokin jihohin kasar, sai ko in matsala ce data shafi kasa baki daya,
Kamar batu daya shafi tsaron kasa, akan wannan zai iya dulmiya kamar yadda doka ta shimfida.

Kamar yadda aka fayyace cikin Dokar Kasa,  Nadawa ko Cire Rawanin Sarki da sauran Shugabanin Gargajiya hurumi ne daya tsaya karkashin Gwamnaticin jihohi, Bai dace ba kuma rashin Da'a ne, 'yan Adawa na Siyasa suyi kokarin alakanta Rikicin jihar kano da Gwamnatin Tarayya da Shugaban kasar Najeriya.

Duk da dai Tsohon General Mai Ritaya, Tsohon Shugaban Gwamnatin Soji, Shugaba Muhammadu Buhari, karara yana da fahimtan karkashin Mulkin Farar Hula na Yanzu, Babbar Gwamnatin Sama (Tarayya) bazata murde ko yin karan tsaye ga Dokokin jiha daya cikin Jihohi da suka dunkule suka zamo Tarayya ba.
Dukkan su sunada ikon su karkashin Dokar Kasa.

Shugaba Buhari ya jinjina wa Al'umman jihar kano kan kasancewa cikin kwanciyar hankali a 'yan kwanakin nan, bayan Sanar da Tube Rawanin Sarki, Yakuma yi Addu'a kan cewa kaddarar Allah kan zone a ko wani lokaci, saboda da haka Masarauta da Al'umman jiha.
A Daina Sa Shugaba Buhari A Rikicin Sarautan Kano A Daina Sa Shugaba Buhari A Rikicin Sarautan Kano Reviewed by MR MB on March 11, 2020 Rating: 5

No comments:

ismaeeelkwr. Theme images by Sookhee Lee. Powered by Blogger.