An fara rusa kasuwar Barci a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna a arewacin Najeriya ta fara aiki war Barci bayan wa'adin da ta bai wa mazauna kasuwar ya cika.
Tun a wayewar garin Asabar din da ta gabata ne mazauna kasuwar suka tarar da takardar wa'adi like gaban shagunansu inda gwamnatin jihar ta umarce su da su tattara su bar kasuwar.
Daraktan Hukumar Kula da Raya Birane ta Jihar Kaduna Ismail Dikko ya shaida wa BBC cewa gwamnatin jihar ta Kaduna na da burin sauya fasalin kasuwar ta yadda jama'a daga kasashen ketare za su rinka zuwa kasuwar domin gudanar da kasuwancinsu.
Ya kuma mayar da martani dangane da korafin da wasu 'yan kasuwar suke yi inda suke cewa an basu wa'adi a kurarren lokaci inda ya bayyana mana cewa doka ta ba su damar bada wa'adi na kwanaki bakwai ko uku.n rushe Kasuwar Barci bayan wa'adin da ta bai wa mazauna kasuwar ya cika.
Tun a wayewar garin Asabar din da ta gabata ne mazauna kasuwar suka tarar da takardar wa'adi like gaban shagunansu inda gwamnatin jihar ta umarce su da su tattara su bar kasuwar.
Daraktan Hukumar Kula da Raya Birane ta Jihar Kaduna Ismail Dikko ya shaida wa BBC cewa gwamnatin jihar ta Kaduna na da burin sauya fasalin kasuwar ta yadda jama'a daga kasashen ketare za su rinka zuwa kasuwar domin gudanar da kasuwancinsu.
Ya kuma mayar da martani dangane da korafin da wasu 'yan kasuwar suke yi inda suke cewa an basu wa'adi a kurarren lokaci inda ya bayyana mana cewa doka ta ba su damar bada wa'adi na kwanaki bakwai ko uku.
'Yan kasuwar barcin sun shaida mana cewa bai kamata a rusa kasuwar ba sakamakon zancen na kotu, sai dai Alhaji Isma'ila Dikko ya shaida mana cewa bai ga wata takarda daga kotu da ta zo ofishinsa ba.
Alhaji Bala Milton, ya shafe kusan shekaru 35 yana kasuwanci a kasuwar barci, ya kuma shaida mana cewa 'yan kasuwar da dama sun shiga cikin wani hali har an kwantar da wasu a asibiti sakamakon kaduwar da suka yi da lamarin.
Tun a ranar Asabar bayan an fitar da sanarwar, sai 'yan kasuwar suka fara tattara kayayyakinsu da balle kofofin shagunansu.
Rahotanni sun shaida cewa a daren Litinin, wayewar garin Talata motocin gwamnati suka shiga kasuwar suka fara rusa ta.
Tun a kwanakin baya ake rade-radin cewa gwamnatin jihar za ta rushe kasuwar domin sauya mata fasali zuwa tsarin kasuwa ta zamani inda tuni aka fara da kasuwar kawo ta jihar

An fara rusa kasuwar Barci a Kaduna An fara rusa kasuwar Barci a Kaduna Reviewed by SAMSONGALAXY.com on March 10, 2020 Rating: 5

No comments:

ismaeeelkwr. Theme images by Sookhee Lee. Powered by Blogger.