El-Rufai ya bai wa Sanusi mukami a Kaduna


Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufai ya bai wa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II mukami a hukumar bunkasa zuba jari ta jihar.
Gwamnan na jihar Kaduna, ya nada Sanusi a matsayin mataimakin shugaba a majalisar magabata ta hukumar bunkasa zuba jari ta jihar wadda ake kira KADIPA, kwana daya bayan da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sauke shi daga gadon sarautar Kano.
Malam Muhammadu Sanusi II ya yi aiki a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, kafin ya zama Sarkin Kano a 2014.
A lokacin ya kawo manyan sauye-sauye a harkar banki da tattalin arziki a Najeriya.
Wata sanarwa daga gwamnatin jihar Kaduna wadda mai bai wa gwamna el-Rufai shawara kan kafofin watsa labarai da sadarwa, Mr Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu, ta ce jihar Kaduna na fatan amfana da 'dimbin basira, da gogewa da kuma sanin jama'a' da Allah Ya hore wa Malam Sanusi domin bunkasa zuba jari da tattalin arziki a jihar Kaduna.
Sanarwar ta kuma ambato gwamna Nasir el-Rufai na cewa martaba ce ga jihar ta samu mutum mai girma irin Sanusi ya jagoraci ci gabanta.
Sauke Sanusi daga matsayin Sarkin Kano da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya yi dai ya janyo cece-ku-ce a ciki da wajen Najeriya.
Tuni aka nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano domin maya gurbin Sanusi.
A halin da ake ciki tsohon Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi II na jihar Nasarawa inda hukumomi suka kai shi bayan da aka sauke shi daga gadon sarautar Kano.
Kawo yanzu ba a ji ta bakinsa ba kan sabon mukamin da gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai ya ba shi.


El-Rufai ya bai wa Sanusi mukami a Kaduna El-Rufai ya bai wa Sanusi mukami a Kaduna Reviewed by SAMSONGALAXY.com on March 10, 2020 Rating: 5

1 comment:

  1. Lucky Club Casino Site in India - Login | Lucky Club.Live
    Lucky Club is an online gambling site established in 2018. With over 400 casino games, we were first luckyclub introduced to the online gambling industry in 2018.

    ReplyDelete

ismaeeelkwr. Theme images by Sookhee Lee. Powered by Blogger.