Sanusi Lamido Sanusi ya kai kara kan tsare shi a Awe

Sanusi Lamido Sanusi ya kai kara kan tsare shi a Awe
 12 Maris 2020
Image copyright SANI MAIKATANGA Sanusi Lamido Sanusi
Image caption Sanusi Lamido Sanusi ya nemi diyyar naira miliyan 50 kan keta alfarmar 'yancinsa da ya ce an yi
Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya shigar da kara gaban wata babbar kotu a Abuja babban birnin Najeriya yana kalubalantar tsare shi da aka yi a jihar Nasarawa bayan sauke shi daga sarautar Kano.

Tsohon sarkin yana karar mutum hudu ne da suka hada da supeto janar na 'yan sandan Najeriya, da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kwamishinan shari'a na jihar Kano da kuma ministan shari'a na Najeriya.

Ya bukaci mutanen da ya shigar kara su biya shi diyyar naira miliyan 50 saboda keta masa mutunci da kuma take hakkokinsa da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi.

A ranar Litinin ne gwamnatin Kano ta sauke tsohon sarkin na Kano, sannan aka mayar da shi jihar Nasarawa, inda aka yi masa daurin talala.

Ya dai bayyana cewa ba zai kalubalanci sauke shi ba, amma ya kalubalanci tsare shi da kuma kai shi wani waje ba tare da son ransa ba.
Daya daga cikin lauyoyin tsohon sarkin Barr. A B Mahmoud ya shaida wa BBC cewa a ranar Juma'a ne kotu za ta zauna domin duba bukatar da suka shigar.

Tsohon sarkin wanda ya yi amfani da Sunan Sanusi Lamido Sanusi wajen shigar da karar maimakon Malam Muhammadu Sanusi II da ya fara amfani da shi bayan ya zama sarkin Kano, ya nemi kotun ta bayyana cewa tsare shi da aka yi a garin Awe na jihar Nasarawa ko wani wajen daban ya saba wa sassan kundin tsarin mulkin Najeriya da ya bai wa kowane dan kasa damar walwala da zama a inda yake so, sai dai idan kotu ce ta ce a tsare shi.

Haka kuma takardar shigar da karar mai shafi 37 ta nemi kotun ta bayyana cewa fitar da shi da aka yi daga Kano bayan sauke shi daga sarauta ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Takardar karar ta kuma nemi kotun ta bayyana cewa cuzgunawa da wulakantawa da jami'an tsaro suka yi wa tsohon sarkin bisa umarnin mutanen da ya kai kara sun saba wa hakkinsa na mutuntaka kamar yadda yake a kunshe a kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokokin nahiyar Afirka.

Kazalika, Sanusi Lamido Sanusi ya nemi kotun ta bayyana cewa ya cancanci a biya shi diyya sannan a nemi afuwarsa a bainar jama'a saboda keta masa alfarma ba tare da bin ka'idojin da doka ta tanada ba.

Baya ga wadannan bukatu, tsohon sarkin ya bukaci kotun ta umarci mutanen da aka shigar karar da su sake shi ba tare da wasu sharuda ba.

Sannan takardar karar ta nemi kotun ta umarci wadanda aka kai kara da su janye duka jami'an da suke tsare da tsohon sarkin.

Takardar karar dai na dauke da sa hannun lauyoyi 45, wadanda 12 daga cikinsu masu darajar SAN ne.

Sanusi Lamido Sanusi ya kai kara kan tsare shi a Awe Sanusi Lamido Sanusi ya kai kara kan tsare shi a Awe Reviewed by SAMSONGALAXY.com on March 13, 2020 Rating: 5

No comments:

ismaeeelkwr. Theme images by Sookhee Lee. Powered by Blogger.